Bangaren kasa da kasa: A yau da gobe ne za a gudanar da taro karo na biyu na kasa da kasa kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci a Musulunci a Kazan fadar mulkin kasar Tataristan.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar Halal Focus ta watsa rahoton cewa; A yau da gobe ne za a gudanar da taro karo na biyu na kasa da kasa kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci a Musulunci a Kazan fadar mulkin kasar Tataristan.
Kimanin wakilan kasashen kudu maso gabacin asiya,yankin gabas ta tsakiya da Turai dari biyar ne suka halarci gurin wannan taro da kuma taron ya tattauna maganar sanya hannayen jari da harkokin banki a musulunce da harkokin saye da sayarwa a fadin duniya.
586945