IQNA

Ana Shirin Kafa Cibiyoyin Kare Hakkokin Musulmi A Danmark

16:48 - July 19, 2010
Lambar Labari: 1958698
Bangaren kasa da kasa; Babban kwamitin musulmin kasar Danmark na shirin kafa wasu cibiyoyi na kare hakkokin musulmin kasar, bisa la'akari da halin da suka samu kansu a ciki a tsakanin al'ummar kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na alukah.net an bayyana cewa, Babban kwamitin musulmin kasar Danmark na shirin kafa wasu cibiyoyi na kare hakkokin musulmin kasar, bisa la'akari da halin da suka samu kansu a ciki a tsakanin al'ummar kasar ta Danmark.

Bayanin ya kara da cewa kwamitin yana kallon daukar irin wannan mataki a mtsayin wani abu da ya zama wajibi, domin kuwa musulmi na fuskantar matsaloli da dama a kasar, tare da danne hakkokinsu kasantuwarsu su ne marassa rinjaye, bugu da karu kuma ga masu nuna musu tsananin kyama saboda addininsu.

616595





captcha