Bangaren kasa da kasa; Kwamitin malaman addinin musulunci na kasa da kasa zai gudanar da babban zamansa a birnin Makka mai alfarma, wanda shi ne karo na biyu da zai gudanar da irin wannan zama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Almadina da ake bugawa a kasar Saudiya ta rubuta a bugunta na jiya cewa, kwamitin malaman addinin musulunci na kasa da kasa zai gudanar da babban zamansa a birnin Makka mai alfarma, wanda shi ne karo na biyu da zai gudanar da irin wannan zama a babban dakin taronsa da ke birnin mai tsarki.
Rahoton ya ci gaba da cewa za a gudanar da zaman taron ne tare da halartar dukkanin mambobin kwamitin, wadanda suka fito daga kasashen musulmi da larabawa.
Daga cikin muhimman abubuwan da zaman kwamitin zai mayar da hanakali kansu har da batun samara da hanyoyi na kara bunkasa ilimi na sanin shari'a da hukunce-hukuncen musuluncci tsakanin al'ummar musulmi.
623779