Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zanatawa da ta hada shi da shugaban kwamitin bunakasa harkokin kur'ani Hamid Muhammad Muhammadi ya bayyana cewa; kwamitin bunakasa ayyukan kur'ani mai tsarki zai gudanar da zamansa a ranar Asabar mai zuwa tare da halartar ministan ma'aikatar raya al'adun Musulunci da kuma wasu daga cikin mambobin babban kwamitin bunkasa harkokin ala'du.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro shi ne irinsa na biyar da wannan kwamiti zai gudanar tun bayan da aka kafa ta, kuma yanzu haka wasu mambobin kwamitin sun kammala hada bayanan da za su gabatar.
Daga wadanda aka gayyata zuwa zaman taro har da wakilai daga ma'ikatu daban-daban na kasa, da kuma wasu wakilai daga hukumar radiyo da talabijin.
639317