Kafanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta mu'assisar kasa da kasa mai kula da gudanar da wannan gasar ya watsa rahoton cewa; makranta kur'ani biyar ne suka yi saura a gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa ta birnin dubai kuma a ranar biyar ga watan shahrivar na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara suka yi saura a gasar karo na tara. Wadanda suka yi sauran su ne Ridvan daga kasar Bangladesh da Alhasan Bayu daga kasar Guinee Bissau,Ahmad Yasiri Muhammad daga kasar masar,Uktafiyo Farnandi daga Mauzambik da kuma Mung Ung Nari daga kasar Miuanmar sune mahardata biyar da suka yi saura a wannan gasar.
642818