Bangaren kur'ani; Bangaren kula da ayyukan addini na jami'oin kasar Iran ya gabatar da wwata shawar ga shugaban kasar Iran, da ke neman a assasa wata rana ta kur'ani ta duniya da za a rika gudanar da tarukan na musamman.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban babban kwamitin da ke kula da ayyukan addini na jami'oin kasar Iran ya gabatar da wwata shawar ga shugaban kasar Iran, da ke neman a assasa wata rana ta kur'ani ta duniya da za a rika gudanar da tarukan na musamman kan kur'ani mai tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kwamitin Mohammad Hossain Yadgari ya bayyana cewa, suna bukatar shugaban kasar Mahmud Ahmadinejad ya bayar da muhimmanci ga ayyukan kur'ani a jami'oi, bayan haka kuma a kafa wata rana da za a yi walakabi da ranar kur'ani ta duniya.
A cikin bayaninsa assasa irin wannan rana nada matukar muhimmanci a bangarori da dama na yada manufofin kur'ani ga al'ummomi na cikin gida da kuma wajen kasa.
Yanzu haka dai mambobin kwamitin na jiran jawabin shugaban kasa kan shawarar da suka gabatar masa da yawun kwamitin.
643907