Bangaren kasa da kasa;an fara gasar hardar kur'ani mai girma da tajwidi da kuma hardar Hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma Sirar ma'aikin kuma a ranar bakwai ga watan Shahrivar ne a garin Nuwakcot fadar mulkin kasar ta Mauritaniya aka fara.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin Mautiya ta watsa rahoton cewa; an fara gasar hardar kur'ani mai girma da tajwidi da kuma hardar Hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma Sirar ma'aikin kuma a ranar bakwai ga watan Shahrivar ne a garin Nuwakcot fadar mulkin kasar ta Mauritaniya aka fara. A wannan gasar karatun Kur'ani mahardata dari da arba'in da biyar ne karkashin sa idon Ahmad Wuld Alnini ministan harkokin addini da koyarwa na Mauritaniya za su fafata da juna a cikin kwanaki uku.
644643