IQNA

An Aike Da Makaranta Iraniyawa Zuwa Kasar Turkiya

11:31 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985727
Bangaren kur'ani; An aike da makaranta Iraniyawa zuwa kasar Turkiya domin gudanar da shirye-shiryen karatun kur'ani mai tsarki da aka saba gudanarwa a kowace shekara a cikin watan Ramadan mai alfarma.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da shugaban hukumar kula da ayyukan kur'ani ta kasa Rahim Khaki ya bayyana cewa, an aike da makaranta Iraniyawa zuwa kasar Turkiya domin gudanar da shirye-shiryen karatun kur'ani mai tsarki da aka saba gudanarwa a kowace shekara a cikin watan Ramadan.

Ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda aka zaba domin su tafi kasar Turkiya, makaranta ne da suka taka gagarumar rawa a bangarori da daban-daban na kur'ani a cikin kasar, kuma sun samu kyakkyawan yabo kan hakan.

Jamhuriyar Musulunci ta saba gudanar da shirye-shirye na kur'ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi, da suka hada da gudanar da karatu a kafofin yada labarai a tsawon watan azumi.


645640




captcha