Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bangare na taron baje kolin kasa da kasa da ake gudanarwa a karo na goma sha takwas an nuna wasu alluna da ke dauke makaloli kan batun holokost da ake zargin an aikata kan yahudawan a kasar jamus a lokacin yakin duniya na biyu karkashin jagorancin Hitler shugaban jamus na wancan lokacin.
Bayanin ya kara da cewa allun suna nuni da ra'ayoyi da suka gino kan dalilai na ilimi da cikaken bincike kan batun holokust, inda ake nuna shakku kan yadda aka kambama lamarin.
646555