IQNA

Baje Kolin Kayayykin Fasahar Musulunci Da Na Kur'ani A Tunisia

11:09 - September 05, 2010
Lambar Labari: 1987556
Bangaren kur'ani; An fara gudanar da wani baje kolin kayayyakin fasahar Musulunci da na kur'ani a birnin Tunis na kasar Tunisia wanda ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya samu daga bangaren hulda da jama'a na ofishin kula da ayyukan al'adu na na iran an bayyana cewa, an fara gudanar da wani baje kolin kayayyakin fasahar Musulunci da na kur'ani a birnin Tunis na kasar Tunisia wanda ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya dauki nauyinsa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron baje koli ya hada abubuwa da dama da suka danganci fasahar Musulunci da kuma fasahohi da suka danganci rubutun kur'ani mai tsarki da dai sauransu.

Daga ciki kuwa har da wasu manyan alluna da aka aka yi zane-zanen ababe na wurare masu tsarki da ake girmamawa a addinin Musulunci, haka nan kuma rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki da aka kawata.

647610



captcha