IQNA

Taron Makon Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Kyrgystan

13:33 - September 05, 2010
Lambar Labari: 1987923
Bangaren kur'ani; An fara gudanar da wani zaman taron makon kur'ani a birnin Beshkek na kasar Kyrgystan wanda reshen cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi na kasar Iran ya dauki nauyin shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da wani zaman taron makon kur'ani a birnin Beshkek na kasar Kyrgystan wanda reshen cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi na kasar Iran ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro da zai dauki tsawon kwanaki bakwai ana gudanar da shi zai mayar da hanakali ne wajen gabatar da laccoci ga masu halartar taron kan ilmomin kur'ani, da kuma abubuwan da yake koyar da musulmi a cikin rayuwarsu ta zamantakewa.

Yanzu haka dai malamai dam asana da dama ne daga sassa daban-daban na kasar suke halartar wannan zaman taro, gami da wasu makaranta kur'ani.

647115

captcha