Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga reshensa da ke tsibirin Kish cewa, an kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a tsibirin na jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da halartar ministan ma'aikatar kula da harkokin al'du na kasar a daren ranar da ta gabata.
Wannan gasar karatun kur'ani tana daya daga cikin irinta da ake gudanarwa a sassa daban-daban na kasar, inda akan gayyaci makaranta da kuma mahardata daga garuruwa na kasar domin su zo su gabatar da karatu ko harda a irin wannan gasa.
Cibiyar kula da yada ayyukan kur'ani takasar Iran ita ce kan dauki nauyin shiryawa da kuam gudanar da irin wannan gasa. Daga cikin wadanda suka zo a matsayi na daya da na biyu da na uku sun samu kyautuka.
651800