Bangaren al'adu da fasaha; Shugaban mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a yankin Jamo na Keshmir ya bayyana kiran da wani baamurke ya yin a kone kur'ani mai tsarki da cewa alamu ne na kawo karshen masu girman kai na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada bangaren yada labaransa na kudu maso gabacin nahiyar Asia da Shugaban mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a yankin Jamo na Keshmir, ya bayyana kiran da wani baamurke ya yi na kone kur'ani mai tsarki da cewa alamu ne na kawo karshen masu girman kai.
Haka nan kuma a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a a yankin Sayyid Hassan Mostafa Musavi ya bayyana cewa kokarin dushe haske Allah da makiya ke yi ba zai yi tasiri wajen raunana addinin Musulunci ba.
652266