Bangaren kur'ani; An gabatar da wani shiri na taimaka ma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Zimbabwe, wanda bangaren kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin Iran da ke kasar zai gudanar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, banagaren hulda da jama'a na ma'aikatar al'adu ta kasar Iran ya habarta cewa, an gabatar da wani shiri na taimaka ma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Zimbabwe, wanda bangaren kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin Iran da ke kasar zai gudanar a nan gaba.
Bayanin ya ce wannan shirin zai samu taimako daga bangaren mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan mazauna kasar ta Zimbabwe.
Daga cikin irin taimakon da za a rika bayarwa har na abinci da kuma samar da wasu guraben ayyuka ta hanayar kafa cibiyoyin kasuwanci.
650744