IQNA

Kur'ani Ya Zama Tamkar Jini Mai Gudana A Cikin Jikin Musulmi

13:30 - September 29, 2010
Lambar Labari: 2003873
Bangaren kur'ani, Kur'ani mai tsarki dole ne ya zama tamkar jinni da yake gudana a cikin jikin muslmi, ta yadda zai zama ayyukansa baki daya sun doru kan umurni da hani na kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga reshensa da ke birnin Qom an habarta cewa, shugaban Jami'ar Al-mostafa (SAW) Ali Reza Arafi ya bayyana cewa, kur'ani mai tsarki dole ne ya zama tamkar jinni da yake gudana a cikin jikin muslmi, ta yadda zai zama ayyukansa baki daya sun doru kan umurni da hani na kur'ani.

Arafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban daliban wannan jami'a a taron komawa karatun hutun rabin sheakara, inda ya ja hankalin dalibai su mayar da hankali wajen yin aiki da koyarwar kur'ani a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwa.

Ya kara da cewa babbar matsalart da musulmi suke fuskanta a cikin rayuwarsu ba ta rasa nasaba da rashin yin aiki da koyarwar kur'ani, wanda shi ne dukkanin shirya take cikinsa.

664824




captcha