Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: A Karon Farko Kasar Malaishiya za ta gudanar dataron shekara shekara na kasa da kasa kan Kur'ani da Hadisi a cibiyar bincike ta kur'ani a Jami'ar Malaya kuma a watan Dai na wannan shekara ne za a gudanar. Wannan takon kasa da kasa da cibiyar binciken kur'ani da akademiya ta binciken Musulunci a jami'ar Malaya ta Malaishiya nada manufar karfafawa da binkasa binciken jami'ar ta fuskar Kur'ani da sauran ilimomi da ked a dangantaka da Kur'ani da kuma a wannan taro za a samu halartar yan jami'a da wadanda suka kammala karatunsu da dama .
669588