Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar Ama ya watsa rahoton cewa: an girmama wadanda suka gudanar da gasar karatun kur'ani a kasar Rwanda a ranar sha uku ga watan Mihr kuma an gudanar da wannan bikin girmama a garin Kigali fadar mulkin kasar. Wannan gasar ta karatun kur'ani an gudanar da ita ne a watan azumin Ramadana kuma mutane tara ne suka samu kyautuka masu armashi a wannan gasar.
669727