Bangaren kasa da kasa: babban filin sabga da tashin jirage na kasa da kasa na birnin Karbala za a gina shi karkashin fasaha da tsari irin na Musulunci.
Kamfanin dillancin labarai Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar labarai na Nun ya watsa labarai cewa; babban filin sabga da tashin jirage na kasa da kasa na birnin Karbala za a gina shi karkashin fasaha da tsari irin na Musulunci.Wannan filin sabkar jirage zai taimaka matuka gaya wajen sabka da tashin jirage a fadin kasar da kuma yankin kuma har ila yau zai taimakawa wajen fito da wannan gari ko shakka babu.
673447