Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da biyu ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira kamariya aka bayyana sunayen wadanda za su jagoranci gasar karatun Kur'ani da tajwidi ta kasa a kasar Katar kuma sakatariyar ma'aiakatar addini ta kasar ce ta bayyana sunayen.
Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar Kabas ta kasar katar ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin da biyu ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira kamariya aka bayyana sunayen wadanda za su jagoranci gasar karatun Kur'ani da tajwidi ta kasa a kasar Katar kuma sakatariyar ma'aiakatar addini ta kasar ce ta bayyana sunayen. Zagayen farko na wannan gasar za a gudanar da shi ne tare da fafatawar mahardata dubu uku da dari daya da sattin da shida kuma ya kumshi bangaren mata da na maza kuma daga ciki dubu daya da dari shida da sattin da bakwai su yi sa'ar zuwa zagaye na gaba.
675280