IQNA

Za A Bayar Da Kyautar Girmamawa Ga Wadanda Suka Shiraya Gasar London

10:50 - October 23, 2010
Lambar Labari: 2017656
Bangaren kasa da kasa: wadanda suka gudanar da gasar karatun kur'ani na birnin London da harda a cibiyar al'adu da Musulunci a London za a girmama su a cikin wani buki na musamman.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta cibiyar Musulunci ta birnin London ya watsa rahoton cewa; wadanda suka gudanar da gasar karatun kur'ani na birnin London da harda a cibiyar al'adu da Musulunci a London za a girmama su a cikin wani buki na musamman. Gasar Karatun Kur'ani mai girma da Harda a cikin watan azumin Ramadana ne aka gudanar tare da taimakon ma'aikatar kula da addini ta kasar saudiya kuma gasar an gudanbar da ita ne cikin kaso biyar.

679937
captcha