IQNA

Bunciken Rawar da Akhalaki Ke Takawa Wajen Yada Ilimi A Duniyar Musulmi

Bangaren kasa da kasa; taron kasa da kasa na bunciken irin tawar da bangaren akhalaki wato kyawawan dabi'u ke takawa wajen yada ilimi a duniyar musulmi kuma a yau ne a kasar Koweit aka fara gudanar da wannan taro karkashin hukumar da ke kula da ilmi da al'adu da koyar ta Musulunci a kungiyar Asesko ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa na bunciken irin tawar da bangaren akhalaki wato kyawawan dabi'u ke takawa wajen yada ilimi a duniyar musulmi kuma a yau ne a kasar Koweit aka fara gudanar da wannan taro karkashin hukumar da ke kula da ilmi da al'adu da koyar ta Musulunci a kungiyar Asesko ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi. Wakilai dam asana harkokin ilimi da al'adu da zamantakewa za su yi dogon nazari da bunciken sanin rawar da bangaren Akhalaki wato kyawawan dabi'u ke takawa wajen yada ilimi a tsakanin musulmi a duniyar musulmi.



682346