Bangaren kasa da kasa: a karon farko za a gudanar da taron kasa da kasa kan karanta kur'ani mai girma da muhimmancin hakan a ranekun ashirin da daya da ashirin da biyu na wannan wata na Aban shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a jami'ar Malaya da ke birnin Kawalampur fadar mulkin kasar ta Malaishiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta CQR ya watsa rahoton cewa; a karon farko za a gudanar da taron kasa da kasa kan karanta kur'ani mai girma da muhimmancin hakan a ranekun ashirin da daya da ashirin da biyu na wannan wata na Aban shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a jami'ar Malaya da ke birnin Kawalampur fadar mulkin kasar ta Malaishiya. Wannan taro zai samu halartar masana da manazarta a bangaren ilimi da harkokin kur'ani a ciki da wajen kasar ta malaishiya inda za su share wadannan kwanaki biyu suna nazari da tunanin yadda za su inganta wannan lamari mai muhimmanci.
686509