IQNA

Musulmi Sun Nuna Adawarsu Kan Cin MutUncin Kur'ani A Atan

15:28 - November 20, 2010
Lambar Labari: 2034444
Bangaren kasa da kasa;Daruruwan mutane ne musulmi da ke zaune a birnin Atan babban birnin kasar Girka a ranar alhamis ashirin da bakwai ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya suka gudanar da zanga-zanga nuna adawarsu da yadda wani dan sanda a kasar ya ci mutuncin kur'ani mai girma.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Dawn ya watsa rahoton cewa; Daruruwan mutane ne musulmi da ke zaune a birnin Atan babban birnin kasar Girka a ranar alhamis ashirin da bakwai ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya suka gudanar da zanga-zanga nuna adawarsu da yadda wani dan sanda a kasar ya ci mutuncin kur'ani mai girma.Karkashin rahoton yan sanda kimanin musulmi dari uku ne mazauna birnin na Atan sun yi tsintsirindo a gaban babban ginin ma'aikatar magajin garin inda suka bayyana rashin jin dadinsu dangane da wannan cin mutunci da aka yi wa kur'ani mai girma.mahukuman ma'aikatar sun karyata batun yaga kur'ani da wani dan sanda ya yi a lokacin da yake rikici da wani dan kasar masar.

697618
captcha