IQNA

Raya Abubuwa Da Fahimta Irin Ta Kur'ani Shi Ne Burinmu

14:28 - November 21, 2010
Lambar Labari: 2035188
Bangaren kasa da kasa; shugaban jami'ar Almustapha (SWA) Al'alamiya ya bayyana cewa fadakarwa da fahimtar da abubuwa masu kima na kur;ani shi ne tushe da burin kungiyoyi da cibiyoyin Kur'ani a wannan jami'ar ta Almustapha (SWA) Al'alamiya da ke birnin Qum.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; shugaban jami'ar Almustapha (SWA) Al'alamiya ya bayyana cewa fadakarwa da fahimtar da abubuwa masu kima na kur;ani shi ne tushe da burin kungiyoyi da cibiyoyin Kur'ani a wannan jami'ar ta Almustapha (SWA) Al'alamiya da ke birnin Qum. Ayatullahi Ali Rida Aarafi shugaban jami'ar Almustapha (SWA) Al'alamiya ta birnin Qum aranar ashirin da tara ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin bude gasar Olyampiq ta kur'ani da hadisai ta kasa da kasa a birnin Qum ya bayyana cewa; bayan taya murna da wannan mako na wilaya da jinjinawa da kuma godiya ga wadanda suka samu dama da lokacin halartar wannnan Olumpiq da kuma zuwa ga wadanda suka shirya to burin shirya wannan gasar shi ne fadakarwa da ilmantar da abubuwa masu kima na kur'ani da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.

698198

captcha