IQNA

Jami'ar London Ce Za Ta Karbi Bakoncin Zaman Koayar Da Tafsirin Suratul Lukman

16:00 - November 22, 2010
Lambar Labari: 2036057
Bangaren kasa da kasa; a ranar sha uku ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya jami'ar birnin London za ta jagoranci zaman bada horo kan tafsirin suratul Lukman.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta iidr ya watsa rahoton cewa; a ranar sha uku ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya jami'ar birnin London za ta jagoranci zaman bada horo kan tafsirin suratul Lukman.Wannan zaman bada horo zamama da babu kibkibtawa da da za a fara daga misalin karfe tara na safiya zuwa karfe shidda da rabi na yamma agogon birnin na London. A wannan zama za a yi nazari kan dalilan sabkar wannan sura ta Lukman da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa dangane da Lukman da kuma nasihar Lukman ga dansa dangane da tauhidi a matsayinsa na tushen dukan ilimi ,Kan uwaye da girmama su ,aikata ayyukan alheri,Girman kan tushen sabo da kuma hanyoyin kubuta daga shi suna daga cikin abubuwan da za a yi nazari a wajen wannan taro.



698733

captcha