Bangaren kasa da kasa: a kasar Turkiya ne aka gudanar da taron sanin irin dangantakar da ke akwai a tsakanin addinin Musulunci da motsa jiki a cikin al'umma kuma a ranar alhamis sha daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya jamai'ar Sakarya ta kasar Turkiya aka gudanar da wannan zama.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta risalehaber ya watsa rahoton cewa; a kasar Turkiya ne aka gudanar da taron sanin irin dangantakar da ke akwai a tsakanin addinin Musulunci da motsa jiki a cikin al'umma kuma a ranar alhamis sha daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya jamai'ar Sakarya ta kasar Turkiya aka gudanar da wannan zama. Wannan taro an gudanar da shi karkashin kulawar jami'ar da ke koyar da ilimin sanin Allah a jami'ar ta Salkariya da kuma manyan shugabannin koyar da motsa jiki a wannan gari tare da halartar malaman jami'ar da kuma talibanta.
705517