Bangaren al'adu da fasaha;gungun mahajjatan Afganistan sun soki yadda aka kula da su a lokacin aikin hajjin bana da cewa gwamnatin saudiya bat a kyautata masu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Afganistan Ava ya watsa rahoton cewa; gungun mahajjatan Afganistan sun soki yadda aka kula da su a lokacin aikin hajjin bana da cewa gwamnatin saudiya bat a kyautata masu ba. Mahajjatan bana daga kasar Afganistan sun bayyana cewa kamar sauran shekarun da suka gabata babu wani banbanci daga birnin Makka har lokacin komawarsu birnin Kabul sun ga rashin adalci da kulawa da alhali kuma ministan ayyukan hajji na kasar Afganistan ya yi masu alkawalin magance matsalolin da suke fuskanta kafin kammala aikin hajjin bana amma babu wani sauyi da suka gani.
705887