Bangaren kur'ani, An fara gudanar da wani zaman taro kan rubuce-rubuce da suka danganci kur'ani mai tsarki a mataki na kasa da kasa a birnin Tehran da aka baiwa taken da nufin kara samar da fagen bincike kan ayoyin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da mai aiko masa da rahotanni ya bayar daga birnin Tehran ya bayyana cewa, an fara gudanar da wani zaman taro kan rubuce-rubuce da suka danganci kur'ani mai tsarki a mataki na kasa da kasa a birnin Tehran da aka baiwa taken da nufin kara samar da fagen bincike kan ayoyin kur'ani mai girma.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da daya daga cikin wadanda suka halarci zaman, kuma babban bako da ya wakilci ministan ma'aikatar kula bunkasawa da raya harkokin al'adu da ilimin musluci Hamid Mohammadi, ya bayyana matukar gamsuwarsa da yadda ake shirya irin wadannan taruka.
Ya ce ko shakka babu gudanar da irin wadannan taruka a matsayi nakasa da kasa, zai taimaka wajen fadada bincike kan ilmomin kur'ani a duniya, tare da kara kiyaye hakinin koyarawar addinin muslunci a tsakanin al'ummomin musulmi.
706750