Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kwaliya ta biya kudin sabulu a gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani ta yan maji'a musulmi kuma haka ya tabbatar da gamsuwar mahukumtan Iran da wadanda suka shirya wannan gasar. Muhammad Niyazi dan shekaru goma sha takwas wakili daga kasar Masar a wannan gasar karatun kur'ani na yan jami'a musulmi karo na uku a lokacin tattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya bayyana cewa; ya jinjinawa wadanda suka shirya wannan gasar da cewa hanyoyin sadarwa da suka yi wa mahalarta wannan gasar tanadi ya yi daidai kuma komi yayi babu wata matsala kuma ya dace da gasar. Ya kara da cewa wannan gasar ta zama shinfida gay an jami'a musulmi wajen canja da masanyan ra'ayi da tunani a tsakanin juna da kuma bangaren kwarewa gami da irin matsalolin da kasashen musulmi ke fuskanta duka suna daga cikin abubuwan da suka tattauna a kai a lokacin gudanar da wannan gasar.
705933