Bangaren ilimi da nazari: A dalilin cika shekaru talatin da daya da cin nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran,ofishin da ke kula da harkoki yada al'adun jamhuriyar Musulunci a Italiya tare da hadin guiwar Eurasia sun shirya taro kan matsayin mata a tsarin Musulunci a Italiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; A dalilin cika shekaru talatin da daya da cin nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran,ofishin da ke kula da harkoki yada al'adun jamhuriyar Musulunci a Italiya tare da hadin guiwar Eurasia sun shirya taro kan matsayin mata a tsarin Musulunci a Italiya. Reshen kamfanin Ikna da ke kasar Italiya ne ya habarto wannan labari kuma za a gudanar da wannan taro ne daga ranar biyu zuwa hudu ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. A gurin wannan taro za a kaddamar da littafai da dama da suka yi bayani da magana kan mata da matsayinsu da nauyin day a rataya a kansa a cikin Musulunci kamar littafin mace da hakkoki da ayyukannta da kuma jawabai masu gamsarwa.
707434