IQNA

Jami'ar Vindarbilit Ce Za Ta Dauki Nauyin Taro Kan Maryam (S)

Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin ga watan aazar na wannan shekara ce jami'ar Vindarblit da ke jahar tuns na kasar Amerika za a gudanar da taron karawa juna ilimi kan Hadarat Maryam (S) a mahangar kur'ani da injila.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar jami'ar ta Vanderbilt News ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin ga watan aazar na wannan shekara ce jami'ar Vindarblit da ke jahar tuns na kasar Amerika za a gudanar da taron karawa juna ilimi kan Hadarat Maryam (S) a mahangar kur'ani da injila. Gudanar da irin wannan taro ko shakka babu zai taimaka ko shakka babu wajen fahimtar mahangar Musulunci da ta kirista da kuma mahangar kur'ani da injila kan Hadarat Maryam ma'aifiyar annabi Isa (AS) kuma gudanar da irin wannan taro zai kara kusanci a tsakanin musulmi da kiristoci a fadin duniya.

707510