IQNA

An Fara Gasar Kasa Da Kasa Ta Kur'ani Ta Said Junaid A Bahrain

16:36 - December 08, 2010
Lambar Labari: 2044798
Bangaren kasa da kasa; a karo na takwas an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa ta said Junaid a Bahrain kuma ana gudanar da wannan gasar ce a cibiyar Musulunci ta Ahmad Alfatih a birnin Manama fadar mulkin kasar ta Bahrain.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar Alwatan ta Bahrain ya watsa rahoton cewa a karo na takwas an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa ta said Junaid a Bahrain kuma ana gudanar da wannan gasar ce a cibiyar Musulunci ta Ahmad Alfatih a birnin Manama fadar mulkin kasar ta Bahrain.Wannan gasar a ranar sha hudu ga watan Azar ne aka fara gudanarwa kuma hadin guiwar kungiyoyi masu yin hidima da kur'ani mai girma a Bahrain ne suka shirya kuma a wannan karon gasar ba ta takaita kawai da hardar kur'ani ba a'a ta shafi bangarori daban-daban na ilimi .Kuma komitin alkalia ya kumshi alkalai da suka fito daga kasashen Yama masar Maroko Saudiya da Baharain.

708092
:
captcha