IQNA

Musulmai Ya Kamata Su Tashi Su Kalubalanci Kafafe Masu Adawa Da Musulunci

Bangaren kasa da kasa; Najib Razak firaministan kasar Malaishiya ya bukaci musulmin duniya da su tashi tukuru wajen kalubalantar kafafen watsa labarai masu nuna tsananin adawa da gaba kan addinin Musulunci kuma su nunawa duniya cewa addinin Musulunci addini ne na hakika day a dace da kowa.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta kasar ta Malaishiya Bernama ya watsa rahoton cewa; Najib Razak firaministan kasar Malaishiya ya bukaci musulmin duniya da su tashi tukuru wajen kalubalantar kafafen watsa labarai masu nuna tsananin adawa da gaba kan addinin Musulunci kuma su nunawa duniya cewa addinin Musulunci addini ne na hakika day a dace da kowa. A ranar sha shidda ga watan azar ne na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin bukin kaddamar da talbijin ta farko ta Musulunci a kasar mai suna hijirat ya yi wannan bayani da cewa su yi takatsantsan da masu tsauran ra'ayin addini da hakan zai bawa makiyan addinin Musulunci damar yin amfani da hakan wajen cutar da addinin da fina-finai nuna kama kan addinin. Har ila yau ya kara da cewa; bai kamata ba musulmi su nuna kasawa a gwagwarmayar da suke yi da makoyan addinin Musulunci na ciki da na waje.

708997