Bangaren kasa da kasa: ofishin ilimi da bincike na lardin Ihsa'a na Saudiya ya aike da wani hukumci na cikin gida day a bada umarnin lura da kai kawon malama da ma'aikata yan shi'a a guraren gudanar da tarurrukan watan Muharrama da makarantu a fadin lardin.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar gidan labarai na Rasid ne ya watsa rahoton cewa; ofishin ilimi da bincike na lardin Ihsa'a na Saudiya ya aike da wani hukumci na cikin gida day a bada umarnin lura da kai kawon malama da ma'aikata yan shi'a a guraren gudanar da tarurrukan watan Muharrama da makarantu a fadin lardin. Daukan irin wannan mataki na nuni ne da yadda ake ci gaba da takurawa yan shi'a a wannan kasa da kuma yadda hatta a wannan wata day a kama musulmi yan shi'a su nuna alhininsu kan zaluncin da aka yiwa Imam Huseini (AS) da iaylan gidansa da kuma sahabbansa mahukumtan Saudiya na takurawa malama yan shi'a da mabiya wannan mazahaba.
709896