IQNA

Jaddada Wajabcin Lura Da Mu'ijizar Ilmi Ta Kur'ani A Tattaunawar Wayewa

13:50 - December 13, 2010
Lambar Labari: 2047344
Bangaren kasa da kasa; Abdalla bin Abdul Aziz Almuslih babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin duniya na masu lura da muijizojin ilimi da ke kumshe a cikin kur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa ya jaddada wajibcin daukan darasi da ilimi daga cikin abubuwa na ban mamaki na ilimi da ke cikin kur'ani a tattaunawa na wayewa da fahimtar juna.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar Saudiya ta Almadina ya watsa rahoton cewa; Abdalla bin Abdul Aziz Almuslih babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin duniya na masu lura da muijizojin ilimi da ke kumshe a cikin kur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa ya jaddada wajibcin daukan darasi da ilimi daga cikin abubuwa na ban mamaki na ilimi da ke cikin kur'ani a tattaunawa na wayewa da fahimtar juna. Ya kuma kara da cewa masana da manazarta musulmi na iya taka rawar gani ta fuskoki da dama da hakan zai taimaka wajen yada addinin Musulunci da kuma fadakar da sauran al'ummomi.

710950
captcha