IQNA

An Fara Taron Komitin Koli Na Malaman Kasar Marokko

Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Agadir na kasar Marokko aka fara gudanar da taron komitin koli na malaman wannan kasa.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta map ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Agadir na kasar Marokko aka fara gudanar da taron komitin koli na malaman wannan kasa.A wannan taro na kwana biyu an samu halartar Ahmad Taoufiq ministan harkokin addini na kasar ta Marokko kuma mamba a komitin kolin na malaman kasar inda mahalarta taron suka yi nazari kan ayyukan da komitin ya gudanar da kuma irin nasarorin day a cimmawa a burin day a sawa gaba kamar yadda aka ayyana a shekara ta dubu biyu da hudu . Har ila yau da tattauanwa kan rawar da malamai ke takawa wajen ciyar da al'ummar musulmi gaba da kuma himmar mu'assisoshi na fadada ilimi da addini a kasar da karfafa dangantaka tsakanin malamai da al'umma.

713558