Bangaren kasa da kasa: sakataren da ke kula da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a Saudiya bayan ya bayyana sunayen wadanda za su halarci bada horo na farko ga alkalan karatun Kur'ani a dabra da gasar karatun kur'ani na kasa da kasa da tajwidi da kuma tafsirin kur'ani a Saudiya musamman da ake gudanarwar a birnin Makka ya bada labarin halartar wakilai goma daga kasashen waje.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; sakataren da ke kula da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a Saudiya bayan ya bayyana sunayen wadanda za su halarci bada horo na farko ga alkalan karatun Kur'ani a dabra da gasar karatun kur'ani na kasa da kasa da tajwidi da kuma tafsirin kur'ani a Saudiya musamman da ake gudanarwar a birnin Makka ya bada labarin halartar wakilai goma daga kasashen waje. Gudanar da irin wannan bada horo ga alkalai a gasar karatun kur'ani da suka fito daga kasashe daban daban na duniya zai taimaka matuka gaya wajen inganta bangaren alkalanci a karatun kur'ani mai girma.
714402