Bangaren kasa da kasa; a karon na hudu za a gudanar da gasar karatun kur'ani da harda gay an makaranta a kasar Bahrain inda yan makaranta dari biyu da hamsin za su halarta kuma za a fara gudanar da wannan gasar ce a ranekun biyar da shida na watan Dai mai kamawa na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Daily News ya watsa rahoton cewa; a karon na hudu za a gudanar da gasar karatun kur'ani da harda gay an makaranta a kasar Bahrain inda yan makaranta dari biyu da hamsin za su halarta kuma za a fara gudanar da wannan gasar ce a ranekun biyar da shida na watan Dai mai kamawa na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. Ya zuwa yanzu yan makaranta dari biyu da hamsin ne masu shekaru daga shekaru bakwai zuwa sha takwas suka yi sa'ar rubuta sunayensu a cibiyar Islah dake birnin Muharak na kasar Bahrain.Kuma gasar ta kwanaki biyu za a fara gada karfe hudu na mare zuwa karfe takwas na dare agogon kasar kuma a gudanar da bukin bayar da kyauta a ranar sha shida ga watan Dai.
714316