Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : Muhammad Khatibi mahardacin kur'ani da kuma Hamid Wali Zade Makarancin kur'ani bayan sun halarci gasar tankade- da rairaya an zabe su a matsayin wakilan Jamhuriyar Musulunci tai ran a gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa ta yan jami'a musulmi . Bayan fafatawa mai zabi a tsakanin yan takara aka zabi wadannan makaranta kurr'ani gudan biyu a matsayin wadanda za su halarci wannan gasar ta kasa da kasa a tsakanin makaranta da mahardata kur'ani na jami'o'in musulmi a daga kasashe daban daban na duniya.
715007