Kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta UMMID ya watsa rahoton cewa; a karo na bakwai za a gudnar da gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa a kasar Indiya inda wakilin jamhuriyar Musulunci ta Iran zai halarta kuma a yau ne daya ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a garin Bupal na kasar ta Indiya. A wannan gasar bayan ya takara makaranta kur'ani da suka fito daga lungunoni na fadin kasar ta Indiya akwai wasu da suka fito daga kasashe daban daban kamar jamhuriyar Musulunci ta Iran ,Pakistan,Britaniya da Jamhuriyar Panama da za su fafata da juna. Kwanaki biyu za a kwashe ana gudanar da wannan gasar da kungiyar kasa da kasa ta Zinatul Kur'an ta shirya karkashin salo daban daban na kur'ani.
715813