Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kasancewa mata a gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani mai girma ta yan jami'a musulmi da kuma yadda aka yi karin abubuwan da za a yi takara a kansu da suka shafi fahimtar kur'ani kamar kiran salla da wake na Musulunci ya daukaka da fito da wannan gasar. Mantaha Ibrahim Keni shugaban kungiyar makaranta kur'ani a Afrika ta Kudu a wata tattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Kur'ani na Ikna ya bayyana haka da kuma jinjinawa wannan gasar ta kasa da kasa ta karatun kur'ani a tsakanin yan jami'o'in musulmi na duniya.
716281