Bangaren kasa da kasa:a ranar shida ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka fara gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa ta birnin Makka na Saudiya inda aka farad a bangaren harda da tafsirin kur'ani mai girma kuma ake watsa wannan gasar da bangaren al'adu ta radiyon kur'ani na kasar ta Saudiya kai tsaye.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan nakaltowa daga jaridar Almadina da ake bugawa a kasar Saudiya ya watsa rahoton cewa; a ranar shida ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka fara gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa ta birnin Makka na Saudiya inda aka farad a bangaren harda da tafsirin kur'ani mai girma kuma ake watsa wannan gasar da bangaren al'adu ta radiyon kur'ani na kasar ta Saudiya kai tsaye.Wannan gasar ana gudanar da ita ne sau biyu a rana da safe da goma marece inda komitin alkalai na wannan gasar bangaren harda da tafsirin kur'ani ke sa ido kan gasar .Dangane da wannan gasar Abdul Aziz bin Mahyal Dine Khuja ministan watsa labarai na Saudiya ya bayyana cewa; wannan gasar radiyon kur'ani na kasar zai watsa ta bakin daya kai tsaye.
719071