IQNA

Jami'oi Na Taka Gagarumar Rawa A Fagen ShiryaGasar Kur'ani Ta Kasa

13:59 - January 17, 2011
Lambar Labari: 2066145
Bangaren ayyukan kur'ani, Dan majalisar dokokin kasar Iran daga lardin Kohrasan a birnin Mashhad ya bayyana cewa, jami'oi suna taka gagarumar rawa wajen shiryawa tare da gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a mataki na kasa da kasa.


A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna da Sayyid Amir Hussain Kadizadeh Hashemi dan majalisar dokokin kasar Iran daga lardin Kohrasan a birnin Mashhad ya bayyana cewa, jami'oi suna taka gagarumar rawa wajen shiryawa tare da gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a mataki na kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar.

Ya ce gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ak agudanar a birnin Mashhad a cikin makonnin da suka gabata babban dalili ne kan hakan, inda jami'oi na lardin Khorasan da sauran yankuna na kasar Iran suka bayar da babbar gudunmawa wajen ganin shirin ya kai cimam nasara yayin aiwatar da shi.

Gasar da aka gudanar a birnin mashhad dai tana daya daga cikin irintavda aka taba gudanarwa a kasar da suka samu babbar nasara, domin kuwa ta samu halartar makaranta da mahardata daga kasashen msuulmi sama da arba'in, da kuma wakilai na cibiyoyin kur'ani da alkalai na kasa da kasa.

Sayyi Amir Hussain dan majalisar dokokin kasar Iran daga lardin Kohrasan a birnin Mashhad ya bayyana cewa, jami'oi suna taka gagarumar rawa wajen shiryawa tare da gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a mataki na duniya.

730785




captcha