IQNA

Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Daliban Jami'a Wata Hanya Ce Ta Hada Kan Musulmi

10:14 - January 23, 2011
Lambar Labari: 2068979
Bangaren kasa da kasa, Abdulbari Mazhabi daya daga cikin mahardata kur'ani mai tsarki da suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani ta Mashhad, wanda kuma shi ne ya wakilci kasar Tunisia a gasar ya bayyana cewa, gudanar da irin wanann gasa wata babbar hanya ce ta samar da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Abdulbari Mazhabi daya daga cikin mahardata kur'ani mai tsarki da suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani ta Mashhad, wanda kuma shi ne ya wakilci kasar Tunisia a gasar ya bayyana cewa, gudanar da irin wanann gasa wata babbar hanya ce ta samar da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi na duniya baki daya.

Ya ci gaba da cewa hakika yadda aka shirya tare da gudanar da wannan gasa ya burge shi matuka. Domin gasace wadda ta samu halartar makarantan kur'ani da mahardata a matsayi na kasa da kasa, kuma ya yaba da yadda aka tarbe su da nuna musu karamci a jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda hakan a cewarsa yana gagarumin muhimmanci wajen bayyana dabiun Musulunci.

An shirya gudanar da wannan gasa ne a birnin Mashhad a karoo na uku, wadda ta ke samun halartar daliban jami'a daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da kuma kasashen larabawa, hard a wasu daga cikin sauran kasashe, amma a wannan karon salon shirya gasar ya sha banbam da sauran da suka gabata a dukkanin fuskoki.
734483





captcha