IQNA

Filin Nuna Fasaha Saboda Goma Ga Fajir A Etiophiya

Bangaren al'adu da fasaha:a daidai lokaci na kuratowar tunawa da lokacin cin nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun Iran a kasar Etiophiya ya ware wani filin nuna fasaha saboda ranekun nasarar juyin juya halin musuluncin.



Kamfanin da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokaci na kuratowar tunawa da lokacin cin nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun Iran a kasar Etiophiya ya ware wani filin nuna fasaha saboda ranekun nasarar juyin juya halin musuluncin. Daga ranar shidda ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a dakin taro na ta'atar da ke birnin adis Abeba fadar mulkin kasar.



735270