Bangaren al'adu da fasaha:a wani zama da aka bawa sunan bincike adabin juyin juya halin Musulunci a Iran da ofishin al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a Armanistan ya shirya a ranar sha biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya kuma a dakin yin nazarin littafai na kasar ne aka gudanar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a wani zama da aka bawa sunan bincike adabin juyin juya halin Musulunci a Iran da ofishin al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a Armanistan ya shirya a ranar sha biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya kuma a dakin yin nazarin littafai na kasar ne aka gudanar. Shugaban wannan dakin yin nazarin littafai na kasar ta Armanistan bayan jinjinawa kan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran yayi nuni da ziyarar day a taba kaiwa Iran da kuma yadda ya ganewa idonsa irin ci gaban da Iran ta samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.
742547