Bangaren harkokin kur'ani : Dalibai yan kasahen waje ashirin da daya ne suka halarci gasar karatul Kur'ani mai girma da hadisin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa da cibiyar ilimi mai zurfi ta imam Khomeini ® da ke karkashin jami'ar al'mustapha (SWA) al'alamiya ta shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Dalibai yan kasahen waje ashirin da daya ne suka halarci gasar karatul Kur'ani mai girma da hadisin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa da cibiyar ilimi mai zurfi ta imam Khomeini ® da ke karkashin jami'ar al'mustapha (SWA) al'alamiya ta shirya.Abdul Rida Sharifi shugaban ofishin harkokin kur'ani da hadisi a cibiyar ilimi mai zurfi na Imam Khomeini ® a wata tattaunawa da kamfanin dillancin Ikna a birnin Qum ya bayyana cewa; a ranar talatin ga watan Bahman zuwa daya ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za dakin taro na Shahid Sadre za a gudanar da taron.
746704