IQNA

Mutanen Kasar Azarbaijan Sun Nuna Rashin Amincewarsu Kan Kyamar Musulunci

18:46 - February 21, 2011
Lambar Labari: 2084267
Bangaren siyasa da zamantakewa, A daidai lokacin da ake ci gaba da nuna kyamar addinin muslunci ta hanayar tsanar hijabi a kasar Azarbaijan, mutanen kasar sun fara saka manyan takardu akan bangaye na nuna rashin amincewarsu da hakan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a Azarbaijan cewa, a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna kyamar addinin muslunci ta hanayar tsanar hijabi a kasar Azarbaijan, mutanen kasar sun fara saka manyan takardu akan bangaye na nuna rashin amincewarsu da hakan.

Bayanin ya ci gaba da cewa al'ummar kasar Azarbaijan wadanda akasarinsu musulmi ne, suna fuskantar matsala daga mahukunta da suke kawar da kansu daga addinin musulunci tare da neman yin koyi da turai, inda suke hana ska hijabin muslunci a makarantu da sauran wuraren gwamnati.

A wannan lokacin da ake ci gaba da nuna kyamar addinin muslunci ta hanayar tsanar hijabi a kasar Azarbaijan, mutanen kasar sun fara saka manyan takardu akan bangaye na nuna rashin amincewarsu da hakan, tare da neman a kawo karshen wannan doka.

750838






captcha