IQNA

An Gano Wasu Bugon Kur'ani Biyu Masu Kuskuren Bugo Da Aka Dakatar

10:15 - March 02, 2011
Lambar Labari: 2089018
Bangaren kasa da kasa:Sheikh Muhammad Husein babban mia bada fata a Kudus da Palasdinu ya sanar da dakatar da yada wasu kur'anai guda biyu da aka buga saboda kuskuren shafukan da suka kumsa ba daidai suke ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Sheikh Muhammad Husein babban mia bada fata a Kudus da Palasdinu ya sanar da dakatar da yada wasu kur'anai guda biyu da aka buga saboda kuskuren shafukan da suka kumsa ba daidai suke ba.Daya daga cikin kur'anai biyu an buga shi ne a mataba'a ta Mansura da ke kasar Masar kuma ya samu amincewar jami'ar Azhar kafin bugawa amma an tsallake shafi na sattin da hudu da shafi na tisi;in da biyar saboda haka aka dakatar da bugawa.


755814
captcha