IQNA

Kawar Da Kauracewa Ga Kur’ani Mai Tsarki Na Bukatar Himmar Masana A Duniya

13:10 - March 02, 2011
Lambar Labari: 2089274
Bangaren kur’ani, Matukar dai kur’ani mai tsarki bai zama jikin dukkanin bangarori na rayuwar mutane ba to lallai an kaurace masa, kawar da wannan kaucewar kuwa na bukar namijin kokari daga masana musulmi a duk inda suke cikin fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Ali sohbatlo daya daga cikin masana a yankin Zanjan ya bayyana cewa, matukar dai kur’ani mai tsarki bai zama jikin dukkanin bangarori na rayuwar mutane ba to lallai an kaurace masa, kawar da wannan kaucewar kuwa na bukar namijin kokari daga masana musulmi a duk inda suke cikin fadin duniya, domin a cewarsa su ne kawai za su iya zaburar da mutane ta hanyyoyi daban-daban domin komawa zuwa ga kur’ani mai tsarki.
Ya ce abin takaici ne yadda ba mayar da hanakali ga koyar da karatun kur’ani yadda ya kamata a cikin makarantu, ta yadda yara za su tashi da cikakkaiyar masaniya kan kur’ani, kama daga karatunsa har ya zuwa sanin ma’anoninsa, wanda kuma hakan ne zai sanya rayuwar zamantakewar jama ta zama rayuwa ta kur’ani, wato yin aiki da shi.
Matukar dai kur’ani mai tsarki bai zama jikin dukkanin bangarori na rayuwar mutane ba to lallai an kaurace masa, kawar da wannan kaucewar kuwa na bukar namijin kokari daga masana musulmi a duk inda suke cikin fadin duniya musamman kasashen musulmi.
756180


captcha